Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da fara tantance tubabbun matasa da suka daina shaye-shaye da aikata laifuka, domin koyar da su sana’o’i da tallafawa ci gaban karatunsu a karkashin shirin Operation Safe Corridor wanda ake kira da “Tsarin Tudun Mun Tsira.”
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya wakilta, ya bayyana cewa manufar shirin ita ce samar da damar dawowa cikin al’umma ga tubabbun matasa ta hanyar horo da sana’o’i, tallafi, da kuma yafewa.
KNSG Profiles 718 Repentant Thugs, 960 Awaiting Under Amnesty
“Za mu koya musu sana’o’i, mu tallafa musu wajen karatu, sannan mu ba su damar sake komawa cikin al’umma su yi rayuwar koyi kamar kowa,” inji Gwamna Yusuf.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirin, Sarkin Shanun Kano, Alhaji Shehu Muhammad, ya yaba da matakin gwamnatin na dakile yawaitar aikata laifuka a tsakanin matasan jihar.
Haka zalika, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa nauyin da gwamnati ta daura musu na tantance matasan ya kara bayyana himmar da gwamnatin ke da ita wajen yakar laifuka da ta’addanci.
Kano Police Command Arrests 24 Suspected Thugs, Weapons
A nasu bangaren wasu daga cikin matasan da za su amfana sun bayyana cewa suna shirye su tallafawa gwamnatin wajen ganin an magance matsalar shaye-shaye da fadan daba a jihar.
Kwamandan Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya shawarci matasan da su zama jakadu na gari wajen jawo sauran ‘yan uwansu su ma su shiga cikin tsarin domin magance yaduwar shaye-shaye da laifuka.
Taron ya gudana a hedikwatar ‘Yan sanda ta Bompai, inda manyan shugabannin hukumomin tsaro da suka hada da NDLEA da Vigilante suka halarta, tare da yabawa shirin gwamnatin na kawar da miyagun dabi’u a tsakanin matasa.