Gwamnatin Jihar Adamawa ta mayar da yara 14 ga iyayensu bayan an ceto su daga wani gungun masu safarar yara da ake zargin wata mata mai suna Ngozi Abdulwahab ke jagoranta.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, wanda mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa Farauta ta wakilta, ya mika yaran ga iyayensu a wani bikin da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Yola ranar Laraba.
First Lady Pledges Support for Anti-Human Trafficking Agency
Bisa bayanin gwamnati, hukumomi tsaro sun fara bincike a Yuli 2025 bayan yawaitar rahotannin bacewar yara a jihar.
Binciken ya kai ga cafke Ngozi wadda ake zargin tana janyo yara masu shekaru tsakanin huɗu zuwa tara da kayan ciye-ciye a shagon kayan abinci da take da shi a unguwar Jambutu, karamar hukumar Yola ta Arewa.
Daga nan ake zargin tana tura yaran zuwa Kudu maso Gabas inda ake sayar da su kan kudi tsakanin ₦800,000 zuwa ₦1.7 miliyan kowanne.
“Wacce ake zargi ta kware wajen safarar yara daga al’ummomin Adamawa zuwa sauran sassan ƙasa tana mai da su tamkar kayan kasuwanci,” inji Farauta.
Farauta ta bayyana lamarin a matsayin “mummuna kuma abin firgita,” inda ta ce za a gurfanar da wadanda abin ya shafa a gaban kotu bisa dokokin kasa da na jihar, wadanda suka haɗa da:
Dokar Hana Safarar Mutane (2015)
Dokar Kare Yara ta Jihar Adamawa
Dokar Kare Mutane Daga Cin Zarafi (2021)
Penal Code
“Ba za mu bari Adamawa ta zama cibiyar safarar yara ba. Za mu kamo su, mu rushe hanyoyinsu, mu tabbatar sun fuskanci hukunci mai tsanani,” in ji ta.
Don rage raɗaɗin iyayen, gwamnatin jihar ta bai wa kowanne daga cikin iyalai 14 Naira 100,000, tare da kayan abinci da sauran kayan tallafi don farfadowa da kuma kafa kanana sana’o’i.
Gwamna Fintiri ya kuma gargadi iyaye kan sakaci, yana mai jan hankali da cewa ba a kamata a bar yara ‘yan ƙasa da shekaru 10 su tafi makaranta ko yawon aiki ba tare da rakiya daga manya ba.
“’Yan Adamawa sune dukiyar mu mafi daraja, kuma ba za mu bari a rage su zuwa kayan kasuwanci ba. Adamawa ba wurin da ya dace da masu safarar mutane ba ne,” inji Fintiri.
Mataimakiyar gwamnan ta yi kira ga iyaye da su dauki tarbiyyar yara da muhimmanci, tana mai bayyana yara a matsayin “ni’imar Allah mafi tsarki.”
Ta kuma bukaci jama’a su rika kai rahoton duk wani abin da ya haura hankali ga hukumomin tsaro cikin gaggawa domin kaucewa sake faruwar irin haka.