Fitattun ‘yan jam’iyyar haɗaka ta ADC da suka haɗa da Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ne suka jagoranci zanga-zangar nuna adawa da matakin hukumar zaɓe mai zaman kanta Inec kan jam’iyyar da suka kira da “Ceto Dimokuradiyyar Najeriya” a yau, Laraba.
Sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka shiga zanga-zangar sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mar da, tsohon gwamnan Osun Rauf Aregbesola, da tsohon gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal, da sauran su.
Kwankwaso directs loyalists to battle ready for violence against 2027 elections
Magoya bayan jam’iyyar da dama daga jihohin ƙasar da mambobin Kwankwasiyya su ma sun halarci taron zanga-zangar domin miƙa wata wasika da ke kunshe da korafe- korafen su ciki har da maganar yin kira ga shugaban hukumar INEC da ya yi murabus.
Zanga-zangar ta fara ne daga Maitama Roundabout a Abuja, inda ta ƙare a hedikwatar INEC.
Masu zanga-zangar na zargin hukumar zaben da yin aiki tare da jam’iyyar APC mai mulki domin kawo cikas ga dimokuradiyyar kasar.
An ga Amaechi yana cikin wata mota yana yi wa masu zanga-zangar jawabi yayin da suke tafiya a titunan babban birnin ƙasar.
ADC, NNPP Reject Electoral Act Amendment Bill 2026
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya nuna hotuna da bidiyo yayin da yake tare da sauran masu zanga-zangar.
BBC HAUSA

