Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ta Lallasa Brentford Da Ci UkuRundunar ‘yansanda ta ƙasar Uganda ta ce tana bincike game da mutuwar wani ɗanƙwallon ɗan Najeriya mai suna Abubakar Lawal, wanda ya faɗo daga saman ginin wani kantin sayar da kayayyaki.
Lamarin ya faru ne a Kampala babban birnin ƙasar.
Ɗanwasan mai shekara 29 ɗan asalin jihar Sokoto ne a arewacin Najeriya, wanda ɗanwasan gaba ne a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Vipers a Uganda.
Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X ta ce ya faɗo ne daga hawa na uku na ginin kantin Voicemall Shopping Arcade ranar Litinin.
Labaran Wasannin Kungiyoyin Kwallon Kafa A Nahiyar Turai
Ya kai wa wata ƙawarsa mai suna Omary Naima ‘yar ƙasar Tanzania ziyara a rukunin ginin lokacin da abin ya faru, a cewar ‘yansanda.
Tuni aka fara yin ta’aziyya da alhinin rashin ɗanwasan, wanda ya fara taka wa kulob ɗin leda tun watan Yulin 2022 bayan ya shafe shekara biyu da ƙungiyar AS Kigali ta Rwanda.
Ƙungiyar Vipers ta ce: “Lawal (mutumin Sokoto) mutum ne na musamman. Yana da zuciya mai kyau. Ya damu da kowa kuma yana taimakawa. Yana da kyauta matuƙa.”
“Muna alhinin mutuwar fuji’a da tsohon ɗanwasanmu Abubakar Lawal ya yi a yau. Muna roƙon Allah ya sauƙaƙa masa,” kamar yadda tsohuwar ƙungiyarsa ta Nasarawa United a Najeriya ta wallafa.
Fitaccen Dan Wasan Dambe A Britania Ya Baiwa Tinubu Kyauta
Ɗanwasan Uganda Mustafa Kizza ya ce: “Abu ne mai wuya mu iya jure rashin Lawal, mutumin kirki mai hazaƙa, mai fara’a. Ba za mu daina kewarka ba.”
Kafofin yaɗa labarai a Uganda sun ruwaito cewa mutuwar Abubakar ta jawo tambayoyi game da haƙiƙanin abin da ya faru.
Tun da farko wasu na cewa ya mutu ne a hatsarin babur, sai dai ‘yansanda na cewa zuwa yanzu ana tsaka da bincike kan abin da ya yi ajalinsa.
“Hukumomi na bincika kyamarar tsaro ta CCTV da kuma bincike na tsanaki domin gano haƙiƙanin abin da ya faru,” in ji sanarwar ‘yansandan a dandalin X.
BBC HAUSA