Hukumar tace fina-finai da Dab’I ta Jahar Kano ta Aiyana Zubairu Musa Balannaji a matsayin wanda yazo na farko a gasar gajerun labarai ta shekarar 2024
Kannywood’s Newest Sensation: Rukky Alim’s Journey to Stardom
Da take bayyana sakamakon gasar a dakin taro na Malam Aminu Kano dake Mumbayya, Farfesa Halima Abdulkadir Dangambo
Wanda Shugaban kwamitin gasar ya bayyana a madadin ta ya bayyana labarin Bahaushiyar Al’ada wanda marubuci Zubairu Musa Balannaji ya rubuta a matsayin wanda ya yi nasara Kuma ya zama na farko cikin labarai 50 da suka fafata a cikin gasar.
Haka kuma, ya bayyana labarin gadon gida saida Horo wanda Danladi Haruna (Zakariyya) ya rubuta a matsayin wanda ya zo na biyu, Sai labarin Hauwa Shehu Mai taken Bahaushe Mai arziki ne a matsayin wanda yazo na Uku cikin labarai 50 da suka fafata a gasar.
http://Hukumar tace Fina finai
A nashi jawabin Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya bayyana farin cikinshi kan yadda gasar ta gudana tare da taya wanda sukayi nasara murna.
Da yake Zubairu Musa Balannaji ya godewa Allah ya yi tare nuna farin cikinshi dangane da wannan gagarumar nasarar da labarinshi ya yi na zama na farko cikin tarin labaran da aka tantance a yayin gasar
Hukumar ta bawa wanda yazo na farko kyautar Naira Dubu Dari Biyar Sai na Biyu Naira Dubu Dari Uku a yayin da ta Uku ta sami kyautar Naira Dubu Dari Biyu.