Daraktan Mulki da Kudi na karamar hukumar Tarauni Alhaji Abdulkadir Muhammad Arabu, tare da shugaban sassa na karamar hukumar, Suleiman Umar sun kammala aikinsu a yau na tsowon shekaru 35.
Tarauni LGA Bids Farewell to Long-Serving Director, HOD
Inda Daraktan Mulki Mai barin Gado ya Mika kujerar Daraktan mulki ga ma’ajin karamar Tarauni kwamared Bello Hassan Durimin zungura.
Yayin da Suleiman Umar ya Mika kujerar sa ta cpo ga shugaban ma’aikata Nazifi Bello shi Kuma ya Mika kejarar ta shugaban ma’aikata ga Tijjani Muhammad Lawan.
K/H Tarauni Ta Yi Alkawarin Aiki Da Kungiyoyin Cigaban Alumma
Sai Kuma ma’ajjin karamar hukumar ya Mika kujerar sa ga kashiyan karamar hukumar Ahmed M Ahmed dukkanin su a matsayin riko.
Alhaji Abdulkadir Muhammad Arabu Wanda ya yi fice wajen gudanar da ayyukansa cikin kwazo, jajircewa, da kishin ci gaban al’umma da ciyar da ma’aikatan karamar hukumar wanda hakan ya taimaka wajen bunkasa ayyukan karamar hukumar Tarauni
A yayin bikin kammala aikinsa, ya mika ragamar kujerarsa ga Ma’ajjin Karamar Hukumar Tarauni kwamared Bello Hassan, a wani taro da aka gudanar a ofishin shugaban karamar hukumar Tarauni.
Alh Abdulkadir Muhammad Arabu ya roko Alumar karamar hukumar Tarauni da ma’aikatan yankin dacewa duk Wanda ya batawa bisa kuskure ya yafemasa idan shi Kuma yace shi dai duk Wanda yabata masa ya yafe
Shugaban K/H Tarauni Ya Rantsar Da Kansiloli Masu Gafaka
Alhaji Abdulkadir Muhammad Arabu da shugaban sassa Suleiman Umar sun godewa Alummar karamar hukumar da shugaban karamar hukumar Ahmed Ibrahim Muhammad sekure bisa hadin Kai da goyen baya Daya basu har suka kammala aikinsu lafiya
A jawabinsa sabon Daraktan rikon na karamar hukumar Tarauni kwamared Bello Hassan yayi Alkawarin yin aiki tukuru wajan Kara farfado da aiyyukan karamar hukumar Tarauni inda ya nemi hadin Kai da goyen ga ma’aikatan yankin da shugaban karamar hukumar domin ya sauke nauyin da aka dura masa
Dayake jawabi shugaban karamar hukumar Tarauni Alh Ahmed Ibrahim Muhammad sekure ya yabawa Tsohon Daraktan mulki Mai barin gado Alh Abdulkadir Muhammad Arabu da shugaban sassa Suleiman Umar bisa yadda suka nuna jajircewar su wajan bashi dukkanin da shawarwari a lokacin daya kama Aikin bayan zabansa a shugabancin karamar hukumar Tarauni
Ahmed Ibrahim Muhammad sekure daganan yayi fatan Alkairi sabon Daraktan Mulki da Kudi na rikon kwamared Bello Hassan a rikon da zaiyi