Wata kotun a jihar Kano zaman ta a miller road Karkashin jagorancin Mai shari’a Fatima Adamu ta kori karar da wadansu ‘yan kasuwa suka shigar suna kalubalantar shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan Kasuwar kantin kwari Ambasada Akasim Ishaq Tatari Wanda aka fi sani da Balarabe Tatari.
Tunda fari dai wadansu mutane bakwai ne suka sanar da cewa sun dakatar da zababben shugaban na katin Kwari saboda wadansu zarge zarge tare Kuma da garzayawa gaban kotun domin shigar da Kara.
Mun Samar Da Masu Tsaro Sama Da 700 A Kasuwar Kwari-Tatari
A zantawar sa da manema labarai Ambasada Balarabe Wanda Kuma shi ne shugaban gidaje kuma shugaban zauren kantin Kwari Tatari ya bayyana nasarar daya samu a matsayin gagarumjn cigaba ga shugabancin kasuwar.
Ya ce lauyan shi Barrister Suraj Said ya samu nasara akan karar da aka shigar akan wadansu zarge zarge guda shida.
“Inda kotun ta ce Zargin na Sun bashi da tushe ballantana makama a don haka ta kori karar”
Ambasada Balarabe ya ce wadancan mutane basu da hurumin dakatar da shi a matsayin zababben shugaban Kasuwar.
An nada shugaban kungiyar Kasuwar Kwari jakadan zaman lafiya
“Ina zargin sun hada Kai ne da iyayen gidan su suna kulle kulle domin ganin bayan mu Kuma ina Zargin dalilin da yasa aka yi mana tayin wancan kujera a daga mu Kuma a buga mu da Kasa”
“Bayan mun samu nasara a matsayin mu na shuwagabannin kungiyar babu rashawa ba cuta ba cutarwa shi yasa suka ja wasu daga cikin exco din mu suka hada clique Suna yasa farfaganda akan muna yin abubuwan da basu dace ba”
Shugaban hadaddiyar kungiyar Kasuwar ta Kwari ya ce wadancan mutane sun yada maganganu na kage wandanda basu da tushe ballantana makaman.
‘Yan Kasuwar Kwari sun yi kira da a magance yawan haraji a Kano
Ya ce dattawan Kasuwar ta kantin Kwari Sun yi kokarin sasanta lamarin amma abun takaicin Sai wadancan mutane suka zagaya suka shigar da karar da aka kora a yau.
Balarabe Tatari yace tun bayan zaben shi a matsayin shugaban Kasuwar ya gudanar da ayyukan cigaba wandanda suka hada da samar da titi Mai kwalta da Kuma magudanan ruwa a wadansu sassan Kasuwar.
“Mun jajirce wajen Samar da abubuwan more rayuwa kamar inganta network din waya Wanda yake haifar da koma baya ga harkokin sadarwa cikin wasu da dama”
Yayi kira ga ‘yan Kasuwar da su zo a hada Karfi wajen ciyar da Kasuwar ta kantin Kwari gaba tare da neman tafiyar dukannin wandanda ya bata wa rai.
Idan zaku iya tunawa a watannin da suka gabata ne wadansu mutane suka sanar da cewa Sun dakatar da Shugaban na kungiyar ‘yan kasuwar kantin Kwari Ambasada Balarabe Tatari