Juventus ta yi watsi da zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan gaban Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, inda ta karkata akalarta zuwa kan takwaransa na Red Devils Joshua Zirkzee, ɗan ƙasar Netehrlands mai shekara 23.
Labaran Wasannin Kungiyoyin Kwallon Kafa A Nahiyar Turai
Manchester City na iya ɗaukar Martin Zubimendi kan farashin fam miliyan 50 inda ta ke sa ran ɗan wasan tsakiyar na Sifaniya da Real Sociedad, mai shekara 25, zai iya cike giɓin da Rodri mai shekara 28 ya bari a tawagar.
Manchester City da Liverpool da Real Madrid da Paris St-Germain duk suna nazarin yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Bayern Munich da Jamus Jamal Musiala, mai shekara 21 a watan Janairu, wanda aka ƙiyasta darajarsa a kan fam miliyan 150.
Za a Mayar Da Filin Wasa Na D/K Sansanin Kano Pillars-Kwamishina
Ruben Amorim yana fatan Manchester United za ta iya sayen ɗan wasan gaban PSG da Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 26, a watan Janairu duk da cewa ɗan wasan na jan hankalin Chelsea da Tottenham da Arsenal.
Wolves ba za ta saurari wani tayi kan ɗan wasanta na Brazil Matheus Cunha, mai shekara 25, a watan Janairu ba, duk da cewa Arsenal da Manchester United sun nuna sha’awarsu kan ɗan wasan.
Juventus na neman dan wasan bayan Ingila Fikayo Tomori, mai shekara 27, daga AC Milan kan kuɗi fam miliyan 20.
Ɗan wasan Everton da Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 27, zai iya ƙulla yarjejeniya da Fiorentina a watan Janairu, duk da cewa Newcastle da West Ham suna zawarcinsa.
Miguel Almiron zai bar Newcastle a watan Janairu inda ƙungiyoyi a gasar Premier da MLS da Saudiyya zawarcin dan wasan na Paraguay mai shekaru 30.
Ƙungiyar Leganes ta La Liga za ta soke zaman aron da ɗan wasan gaban Ivory Coast Sebastien Haller, mai shekara 30 ke yi a kulob ɗin, domin mayar da shi Borussia Dortmund a watan Janairu.
Manchester United na nazari kan golan Royal Antwerp da Belgium na ƴan ƙasa da shekara 21, Senne Lammens, mai shekara 22.
Liverpool za ta iya sayar da golan Jamhuriyar Ireland Caoimhin Kelleher, mai shekara 26 a bazara mai zuwa idan har ta samu tayi mai tsoka, inda Newcastle bibiyar ɗan wasan.
Ɗan wasan Galatasaray da Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 32, wanda a halin yanzu y ke zaman aro a Lyon, zai iya komawa Amurka inda ƙungiyoyin gasar Major League Soccer ke zawarcinsa.
BBC HAUSA