An bayyana kuɓutar da yara da aka kama kan zargin zanga-zanga da abu mai kyau.
Shugaban Cibiyar Bunƙasa cigaban al’umma, (CDE) Amb. Ibrahim Waiya ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, inda yace wannan abu ne mai kyau kuma musamman duba da yadda shugabannin kowane ɓangare suka haɗa kai duk da bambance bambancen jam’iyya don ganin sun kuɓutar da waɗannan yara a matsayin su na ƴan Kano.
Amb. Waiya ya ƙara da cewa ajiye bambancen jam’iyya don kawowa al’ummar jihar Kano cigaba shine babban abinda suke buƙata a yanzu domin bunƙasa cigaban al’umma musamman ƴan asalin jihar Kano.
Waiya yayi kira da wakilan al’ummar jihar Kano a birnin tarayya da su dafawa gwamnan jihar Kano don ganin a kawowa al’ummar jihar Kano cigaba mai ɗorewa matsayin su na wakilan al’ummar jihar Kano.