Samuel Morrison, mai laƙabin waƙa, Yung Sammy, ya yi fice a fagen waƙoƙi a kasar India, in da a yanzu haka ya ke yin waƙoƙi da yarukan ƙasar.
CNN ta rawaito cewa an haifi Morrison a Nijeriya amma sai su ka koma India yana ɗan shekara 12.
Da ya fara tasawa a ƙasar, kawai sai ya shiga fagen waƙoƙi, babban burin sa a duniya, inda al’umma ya yi fice.
A yanzu haka Yung Sammy ya kware a yarukan Punjabi, Gujari, da Haryanvi kuma da su ya ke rera waƙoƙi a ƙasar da har ya dace zuciyar miliyoyin masoya.