Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa nan kadan ba da dadewa ba zata sabuntawa masu aikin tsaftace tituna kayan aiki a wani yunkuri na Kara sauya fasalin ayyukan masu shara da kyautata jindadinsu.
Kano to Spend NB33.45 on Infrastructure, Edu, and Healthcare
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayi na jihar kano Dr Dahiru Mohammad Hashim ne ya sanar da hakan lokacin da yake jagorantar kaddamar da biyan masu tsaftace tituna kudaden su na wata tara Wanda Gwamnatin Kano Karkashin jagorancin Alh Abba Kabir Yusuf ya sahale a biya su.
Taron Wanda ya gudana a babban dakin taro na coronation Hall dake gidan Gwamnati, Wanda Kuma Ma’aikatan tsaftace tituna kimanin su 2,369 suka amfana da wannan tagwomashi.
New Commissioner Vows to Transform Kano’s Environment
Kwamishinan yake Gwamnati da damu kwarai da irin halin da masu tsaftace tituna suka shiga tsawon lokaci, sai dai yayi musu albishirin cewa daga wannan watan da zarar ko wane maaikaci yaga albashinsa to suma insha Allah zasu GA nasu haka, ya Kuma buka cesu dasu Saka wannan karamci na Mai Girma Gwamna ta hanyar zage dantse da yin aiki tukuru don tabbatar da ingantacciyar tsafta a duk fadin jihar kano.
Dr Hashim ya Kara da cewa Ma’aikatar sa za a fito da tsari na karrama duk maaikacin sharar da yafi nuna kwazo a wajen aikin sa, ta hanyar bashi kyaututtuka da takardar karramawa don kara masa Kai mi.
Jigawa Govt Reviews Environmental Policy For Sustainable Devt.
Daga nan ya jagoranci Mika musu katin cirar kudi na ATM, inda yace zasu iya zuwa ko ina domin su cire kudin su kamar kowa.
Anasa jawabin tun da farko Mai bawa Gwamna shawara akan harkokin Muhalli Engr. Abdullahi Shehu Bichi ya bayyana gamsuwa da wannan tsarin inda ya ja kunne su dasu fitar da Gwamna da Kwamishina kunya ta hanyar yin aiki tukuru, ya Kuma jinjinawa gwamnatin saboda sauke wannan nauyi adaidai wannan lokaci tare da yi musu Karin kudin sabanin abinda Gwamnatocin baya ke basu.
Babban Sakataren kula da hukumar data ke kula da harkokin zaizayar Kasa da sauyin yanayi ta jihar kano Dr Mohammad S. Khalil da takwaransa Managing Director na hukumar kula da gyara da Kuma tsaftace magudanan ruwa na cikin gari Alh Sulaiman Saiki Aliyu Madobi da Kuma Mataimakin Babban Manajan kula da kwashe shara ta jihar kano wato Alh Lamin Mukatar Hassan da Kungiyar nan ta FAO nadaga cikin wadan da suka mika sakon fatan alheri a wannan taro.
Daga bisani Wadan da suka amfana da shiri wato Saude Abdullahi da Kwamandan dakarun askarawan Kwankwasiyya Saminu Balago Yakasai sun nuna farin cikin su tare da alkawarin cigaba da jajircewa wajen aikin da aka dora musu.