Majalisar Dokokin Jihar Kano, karkashin jagorancin Kakakinta, Jibril Ismail Falgore, ta dakatar da yunkurin tsige tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo, bayan murabus dinsa daga mukaminsa.
A zaman majalisar da aka gudanar karkashin jagorancin Falgore, an karanta takardar murabus da Gwarzo ya aike, wadda ta nuna cewa murabus dinsa ya fara aiki ne daga ranar 27 ga Maris, 2026, bisa tanadin Sashe na 306(2) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara).
Majalisar Kano Ta yi Watsi da Karya da ake yadawa akan hutun ta
A cikin sanarwar da mai magana da yawun Kakakin Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar, an bayyana cewa wasikar murabus din ta kunshi cewa: “Ni, Aminu Abdulsalam Gwarzo, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, ina mika takardar murabus dina na son rai daga mukamina, wanda zai fara aiki daga ranar 27 ga Maris, 2026.”
Tun da farko, Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawal Hussain Dala, ya shaida wa manema labarai cewa majalisar ta janye tuhumar tsige shi ne sakamakon murabus dinsa.
Ya kara da cewa, batun duk wani zargi da ake yi masa ya rage ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kamar Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) da Independent Corrupt Practices Commission (ICPC).
Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Musanta Rahoton Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamna
“Ba mu EFCC ko ICPC ba ne; muna sauke nauyin da ke kanmu ne a matsayinmu na majalisar dokoki,” in ji shi.
A wani bangare kuma, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Kiru ya sanar da sauya sheka daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa African Democratic Congress (ADC), yana mai cewa matakin ya biyo bayan rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar.
Har ila yau, majalisar ta karbi rahoton kwamitin binciken kananan hukumomi na shekarar da ta kare a ranar 31 ga Disamba, 2024, wanda Tukur Muhammad Fagge ya jagoranta, inda ya yabawa mambobin kwamitin kan jajircewarsu.
Bugu da kari, shugaban kwamitin harkokin ilimi mai zurfi, Abdulhamid Abdul Minjibir, ya gabatar da kudirin kafa Kwalejin Ilimi da Nazarin Shari’a a Minjibir, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen bunkasa ilimi da rage cunkoso a birnin Kano.
A jawabinsa na maraba bayan hutun Sallah na makonni hudu, Kakakin Majalisar ya taya Abba Kabir Yusuf da al’ummar jihar murnar kammala azumin watan Ramadan da bikin Eid-el-Fitr, yana kira ga jama’a da su ci gaba da riko da kyawawan dabi’u domin inganta zaman lafiya da ci gaban jihar.

