Majalisar Dokokin Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu kafafen yada labarai, wadanda ke nuni da cewa majalisar na shirin tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Musanta rahoton ya fito ne daga bakin Mai Magana da Yawun Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Kamaluddeen Sani Shawai, yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Malam Ali ya samu injin faci daga Dan Majalisar Fagge bayan kuka a kafafen sada zumunta
A cewar Shawai, majalisar na gudanar da dukkan ayyukanta ne a bude, cikin gaskiya da rikon amana, ba tare da boye-boye ko kumbiya-kumbiya ba.
Ya bayyana cewa babu wani shiri ko tattaunawa a halin yanzu dangane da tsige Mataimakin Gwamnan, kamar yadda ake yadawa.
Ya kara da cewa majalisar na ci gaba da gudanar da ayyukanta na yau da kullum bisa tanadin kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, inda ya bukaci al’umma da su yi watsi da jita-jitar da ke yawo a kafafen yada labarai.
Majalisar Kano Ta Nuna Rashin Gamsuwa Da Gyaran Asibitin Nas
Kamaluddeen Shawai ya jaddada cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano za ta ci gaba da aiki bisa gaskiya da bin doka domin ci gaban jihar.

