Jam’iyyar APC ta buƙaci ɓangaren jam’iyyar ADC da tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ke jagoranta da ya bi doka da ƙa’ida, tare da daina yaudarar ‘yan Najeriya kan rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar.
Sakataren ƙasa na APC, Ajibola Basiru, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Juma’a, inda ya jaddada cewa dole ne a mutunta dokoki da ƙa’idojin siyasa.
Basiru ya kuma yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi na a sauke shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Joash Amupitan, da sauran kwamishinonin hukumar, yana mai cewa irin wannan buƙata ta saɓa wa dimokuraɗiyya da kundin tsarin mulki.
A nata ɓangaren, INEC ta bakin kwamishinanta na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai, Mohammed Haruna, ta bayyana cewa matakin da ta ɗauka ya yi daidai da umarnin kotu na ci gaba da riƙe yadda al’amura suke har sai an yanke hukunci na ƙarshe.
Jam’iyyar ADC dai na fama da rikicin shugabanci tun shekarar 2025, bayan bayyanar sabon Kwamitin shugabancin na ƙasa karkashin jagorancin David Mark a watan Yuli na waccan shekarar.
Rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan wa’adin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ralph Nwosu, wanda ya ƙare a watan Agustan 2022. Duk da haka, ya taka rawa a sauyin shugabanci da aka yi a 2025, lamarin da ya haddasa sabani a cikin jam’iyyar.
Sai dai David Mark da sakataren yaɗa labarai na ADC, Bolaji Abdullahi, sun zargi APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da hannu a rikicin.
Da yake mayar da martani, sakataren yaɗa labarai na APC, Felix Morka, ya yi watsi da zargin, yana mai cewa matakin da INEC ta ɗauka ya samo asali ne daga sahihin hukuncin kotu kuma ya yi daidai da dokokin zaɓe.
Daily Nigerian Hausa

