Amadadina dasauran mazauna Unguwannin Yanlemo dake Na’ibawa kantitin zuwa Zaria, ina jawo hankulan Mahukuntan Gwabnati (Hukumar Lafiya, Hukumar kula da Mahalli da Kwashe Shara da Hukumar bada Ruwansha) ta Jihar Kano dasuyiwa Allah suyiwa Annabi (SAW) su:

1.Kawo ziyarar aiki Kasuwar Yanlemo wajen tara Sharar cikin Kasuwa domin daukar matakan dasuka dace domin kare abubuwan daka iya faruwa awannan yankin.

2. Kula dacewa akarkashin wajen zuba Sharar akwai CIBIYAR RUWA dake bawa wannan Unguwanni Ruwansha dana amfani dashi yau dakullun.

3. Duk lokacin da Manyan Motocin kwashe Shara sukayi aiki awajen saisun FASA Bututun Ruwan dake bawa Unguwanni Ruwa.

4. Duk lokacin da’aka samu hakan, Muhukunta bazasuyi kokarin gyarawaba sai lokacin dasukaga damar yinhakan.

5. Idan Allah (SWT) Yasa angyara kuma, Ruwan yanazuwa agurbace da Kasa dakuma tarkace Balar.

5. Ayanzu haka, KWANA DA KWANAKI babu Ruwansha a wannan Unguwar sanadiyyar kwashe sharar datayi sanadiyyar fasa Bututun ruwan.

Dan haka inabada shawara da’a GAGGAUTA daukar matakan GYARA kafin BARKEWAR CUTUTTUKA kamar ZAZZABIN CIZON SAURO, AMAI DA GUDAWA, CIWON FATA dasauransu.

Haka kuma yana dakyau idan zaiyiwu acanza inda za’a dinka tara Sharar ta Kasuwar Yanlemo zuwa wani bangaren. Kokuma asan abinda yakamata ayi wajen kare Bututun ruwan dake kasa.

Dafatan wadanda akayi kiran dominsu zasu amsa kira.

ABDULLAHI YAKUBU MAIKUDI

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version