Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya na samun tallafin ƙasashen waje domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da kuma fashi da makami a sassa daban-daban na ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne cikin saƙon Easter na shekarar 2026 da ya fitar a ranar Juma’ar Good Friday, inda ya amince cewa duk da ƙoƙarin da dakarun tsaro ke yi, har yanzu ana fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu yankuna.
A cewarsa, gwamnatinsa na ci gaba da samar da kayan aiki da abubuwan da ake buƙata, tare da ƙulla haɗin gwiwa da ƙasashen waje domin bai wa jami’an tsaro damar kai farmaki ga ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
Sai dai shugaban bai bayyana sunayen ƙasashen da ke bayar da tallafin ba, haka kuma bai fayyace irin taimakon da ake samu daga gare su ba.
Tinubu ya ƙara da cewa, duk da cewa matsalolin tsaro na nan daram, akwai ci gaba da ake samu sakamakon matakan da gwamnati ke ɗauka, yana mai nuna kwarin gwiwa cewa za a shawo kan matsalolin.
Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun hare-hare a wasu sassan ƙasar, ciki har da kisan gillar da aka yi a baya-bayan nan a Jihar Plateau.
Haka kuma, shugaban ya ce shugabannin hukumomin tsaro sun ba shi tabbacin cewa ayyukan da ake gudanarwa na inganta a filin daga.
Daily Nigerian Hausa

