Manajan Daraktan Gidan Rediyon Jihar Kano, Kwamaret Abubakar Adamu Rano, ya bayyana aniyarsa ta farfado da martabar gidan rediyon .

Abubakar Rano ya jaddada cewa aikin gidan Radio Kano ya wuce yada labarai da shirye-shirye kawai; yana aiki a matsayin wata cibiyar koyar da aikin jarida.

Rano ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar bakuncin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen Kano, a ziyarar ban girma da shugaban kungiyar, Kwamared Sulaiman Abdullahi Dederi ya jagorancin yan tawagarsa suka kai gidan Radio Kano.

Bugu da kari, ya bayyana cewa manufarsa ita ce mayar da gidan Radio zuwa babbar cibiyar ilmantarwa da bunkasa sana’ar yada labarai.

Abubakar Rano ya kuma bayyana cewa gidan rediyon Kano ya zarce takwarorinsa da dadaddiyar tarihin aikin yada labarai a Arewacin Najeriya, inda ya ce an kafa gidan Radio tuna tun kafin Najeriya ta samu ‘yancin kai.

“Don cimma burina, na tsara ayyuka da yawa, ciki har da tabbatar da tafiyar da gidan Radio Kano bisa ka’idojin aikin jarida da baiwa ma’aikata horo akai-akai da samar musu da walwala da dai sauransu.”

“Radiyon Kano za ta ci gaba da rike kambunta na uwa ma bada mama a cikin takwarorinta kafafen yada labarai dake Arewacin Najeriya,” in ji shi.

A yayin da ya bukaci sabbin shugabannin kungiyar ta NUJ da su maida hankali wajen baiwa mambobinsu horo, Inda ya yi nuni da cewa, a kokarin cimma burinsa, ya samar da cibiyar horar da aikin jarida mai inganci a gidan Radio Kano.

“Za mu baiwa kungiyar NUJ cibiyar kyauta domin ta horar da ‘ya’yan kungiyar a kowane lokaci.”

“Cibiyar tana da kayan aikin na IT, na’urar sanyaya iska, da sauran kayan aikin yada labarai .”

Rano ya ce “Kofata a bude take a kodayaushe domin ci gaba da ci gaban aikin jarida.”

Tun da farko, Shugaban kungiyar yan jaridu ta ƙasa reshen jihar Kano, Kwamared Sulaiman Abdullahi Dederi, ya ce shugabannin NUJ sun ziyarci gidan rediyon Kano ne domin nuna jin dadinsu da tallafin da MD ya ba su.

Ya ce, “A yau, ni Sulaiman Abdullahi Dederi, shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Kano, ina so mu mika godiyarmu ga Manajan Daraktan gidan rediyon Kano bisa irin goyon bayan da ya ba mu a lokacin yakin neman zabe da kuma bayan rantsar da mu”.

“Jagorancin ku ya taimaka mana wajen cin nasararmu, kuma muna godiya da jajircewar ku don ci gabanmu. Muna fatan zaku taimaka mana don aiwatar da ajandarmu guda biyar don inganta matsayin aikin jarida a Kano,” in ji shi.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version