Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya baiyana yiwuwar sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa ADC, yana mai danganta hakan da rikicin da ke ci gaba da addabar jam’iyyarsa ta yanzu.
Mohammed, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake karbar bakuncin tawagar jam’iyyar ADC karkashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, a Fadar Gwamnatin Jihar Bauchi.
Da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri, gwamnan ya ce yiwuwar sauya shekar tasa na da nasaba da rarrabuwar kawuna da ta ki ci ta ki cinyewa a cikin PDP, duk da kokarin sulhu da aka yi.
Ya ce kwamitoci a matakin ƙasa da na jiha sun duba dukkan hanyoyin warware matsalar, ciki har da tuntubar jam’iyyar APC, amma duk irin waɗannan ƙoƙarin ba su haifar da nasara ba.
Mohammed ya ƙara da cewa, duk da cewa ana ci gaba da tattaunawa da wasu jam’iyyun siyasa daban-daban, ADC ce ta fi bayyana a matsayin zabin da ya fi dacewa a halin yanzu.
Gwamnan ya kuma zargi cewa rikicin cikin gida da ke addabar PDP na samun karfi ne daga wasu tasirin waje, inda ya zargi Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da taimakawa wajen haddasa matsalar.
Ya kara da cewa ya tuntubi manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin APC da kuma Shugaba Bola Tinubu, domin nemo mafita ga rikicin, amma har yanzu ba a samu warware matsalar ba.
Daily Nigerian Hausa

