Gwamnatin Tarayya ta ba wa ‘yan kasuwar da gobarar da ta auka kwanan nan a Kasuwar Singer a Jihar Kano ta lalata sassa na kasuwar, jimillar Naira biliyan 5, don tallafawa wadanda abin ya shafa.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima,ne ya sabar da hakan yayin ziyarar jaje da ya kai kasuwar a madadin Gwamnatin Tarayya.
Ziyarar ta biyo bayan gobarar da ta faru makon da ya gabata, wadda ta lalata kayayyaki da kadarori masu darajar miliyoyin nairori.
Shettima ya bayyana gobarar a matsayin babban masifa ta ƙasa, inda ya ce ba kawai asara ce ga Jihar Kano ba, har ma ga tarayyar Najeriya baki ɗaya.
Mataimakin Shugaban Kasa, wanda ya samu rakiyar Gwamnonin Jigawa, Kebbi, da Imo, ya yi addu’o’i ga wadanda abin ya shafa, tare da roƙon Allah ya kare a gaba daga irin wannan masifa.
A jawabin sa, Junaid Zakari, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Singer, ya gode wa Gwamnatin Tarayya bisa wannan taimako na gaggawa domin rage radadi ga wadanda iftila’in ya afkawa.
Ya tabbatar cewa za a yi amfani da kuɗin domin tallafawa ‘yan kasuwa da kuma farfado da harkokin kasuwanci a kasuwar.
Wannan mataki na Gwamnatin Tarayya ya nuna kokarin ta wajen rage mummunan tasirin gobarar da tallafawa dawowar tattalin arziki ga al’ummar da abin ya shafa.

