Jamila Sulaiman
An ja hankalin al’umma da su kara aikata ayyukan alkhairi domin cin gajiyar falalar da ke cikin watan Ramadan mai albarka.
Sheikh Nasir Albani PRP ne ya yi wannan kira a yayin rabon kayan abinci da na Sallah da al’ummar unguwar Jaba suka gudanar, bayan sun tara kudade domin tanadin tallafi ga masu karamin karfi a watan Ramadan.
Malamin ya bayyana cewa wannan shiri babban tagomashi ne ga al’ummar yankin, musamman daliban makarantar Bint Hameed Markaz Azzarmawiy, wadanda suka tara kudi da kokari domin tallafa wa raunana a wannan lokaci na tsadar rayuwa.
Shugaban makarantar, Malam Musa, ya bayyana farin cikinsa kan kokarin daliban makarantar, yana mai cewa wannan ya nuna kyakkyawan tarbiyyar da suke samu.
Sai dai ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka wajen samar da ruwan sha a makarantar, yana mai cewa rashin ruwa shi ne babban kalubalen da suke fuskanta.
A nata bangaren, Malama Hajara Abdullahi, wacce ta assasa masallaci da makarantar Bint Hameed Markaz Jaba a karamar hukumar Fagge, ta ce farin cikinta ba zai misaltu ba ganin yadda aka tallafa wa iyayen marayu 60 da kuma yara marayu kusan 40 da kayan abinci da kayan Sallah.
Ta kuma yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su taimaka wajen tallafa wa makarantar domin ta kara bunkasa.
Wasu daga cikin iyayen marayun da suka amfana da tallafin, ciki har da Hauwa Ayuba da Umman Ahmad, sun nuna matukar farin ciki da wannan tallafi da suka samu na kayan abinci da kayan sawa ga ‘ya’yansu.
Sun kuma yi fatan sauran Musulmi, musamman masu karamin karfi, su yi koyi da wannan kyakkyawan aiki na daliban **Markaz Azzarmawiy** da ke unguwar Jaba.

