Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi rashin mahaifiyarsa, Hajiya Umma, wadda ta rasu a ranar Juma’a.
An tabbatar da rasuwar ne cikin wata sanarwa da iyalan El-Rufai suka fitar a ranar Juma’a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Read also: AI Deepfakes, Voice Cloning: NITDA Warns Nigerians of Cyber Threats
Read also: Terrorism: Kebbi Court Jails Two Convicts 15 Years Each
Majiyoyi sun bayyana cewa marigayiyar ta dade tana fama da matsalolin lafiya da suka shafi tsufa, waɗanda suka ƙara tsananta a ‘yan kwanakin nan.
Read also: NSC Inaugurates Four Sports Federation Boards
A cewar majiyoyin, yanayin lafiyarta ya ƙara tabarbarewa bayan ta samu labarin tsare ɗanta da hukumar ICPC ta yi.
Daily Nigerian Hausa

