Ƙasar Saudiyya ta sanar da wata sabuwar doka ta mayar da kashi 50 cikin 100 na ma’aikatan ma’aikatun hada-hadar kuɗi masu zaman kan su guda 17 su kasance ƴan ƙasa ne.
Sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki daga ranar 23 ga watan Mayun 2027.
Read also: From Free Maternity Care to Modern Veterinary Clinics: Kano’s 2027 Dev Agenda
Ma’aikatar Albarkatun Ɗan’adam da Ci Gaban Al’umma ta Saudiyya (MHRSD) ce ta sanar da matakin a ranar Lahadi, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ƙwararrun Akantoci da Masu Lissafin Kuɗi ta Saudiyya (SOCPA).
Read also: NUPRC Prioritises Workers’ Development for Improved Productivity
MHRSD ta ce an ɗauki wannan mataki ne da nufin samar da ƙarin guraben aiki ga ‘yan ƙasar Saudiyya, tare da ƙara yawan shigarsu cikin ma’aikata a kamfanoni masu zaman kansu.
Ta ƙara da cewa matakin zai shafi kamfanoni masu zaman kansu da ke da ma’aikata biyu ko fiye da haka a cikin sana’o’in kuɗin da aka ayyana.
Read also: 67th NCH: Stakeholders Seek Sustainable Health Financing
Za a buƙaci waɗannan kamfanoni su tabbatar sun cika ƙa’idar mayar da yawan ma’aikatan zuwa kashi 50 cikin 100 ga ‘yan ƙasar Saudiyya, bisa sharuɗɗa da tsarin ƙididdigar da ma’aikatar ta tanada dokar.
Biz Point

