Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi barazanar fasa Filin Wasan Yakubu Gowon da ke Port Harcourt idan Gwamnatin Jihar Rivers ta ci gaba da hana shi da magoya bayansa damar gudanar da gangamin siyasa.
Wike ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da shugabannin sanatoci da ƙananan hukumomi na ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors, wacce ke goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓukan 2027.
Jaridar Vanguard ta rawaito Wike na cewa ƙungiyarsa ta nemi izinin amfani da filin wasan amma aka ƙi amincewa, yana mai cewa hakan ba abin yarda ba ne.
Ministan ya jaddada cewa an fara gangamin siyasa a hukumance, yana kuma zargin gwamnatin jihar da rashin nuna cikakken goyon baya ga Tinubu.
Daily Nigerian Hausa

