Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta yi gargaɗi ga ’yan Najeriya kan yaduwar kwaroron roba na Kiss na bogi a manyan kasuwanni a faɗin ƙasar.
A wata sanarwa da ta fitar, NAFDAC ta ce ta samu bayanan ne daga DKT International Nigeria, inda aka gano kwaroron roban bogin a kasuwanni kamar Onitsha, Idumota, Trade Fair, da kuma wasu sassan Kano, Abuja, Uyo, Gombe da Enugu.
Hukumar ta bayyana cewa kwaroron roban bogin na da ƙarancin inganci, rashin tsafta, ƙarancin man shafawa da kuma kuskuren bayanai a jiki, lamarin da ke jefa lafiyar masu amfani cikin haɗari.
Ta ce amfani da irin waɗannan kayayyaki na ƙara barazanar kamuwa da cututtuka da rashin kariya yadda ya kamata.
NAFDAC ta umarci ofisoshinta na jihohi da shiyyoyi da su ƙara sa ido tare da kwashe kayayyakin bogin daga kasuwanni.
Haka kuma, ta shawarci ’yan kasuwa da jama’a da su sayi kayayyakin lafiya ne kawai daga masu izini, tare da kai rahoton duk wata shakka ga ofishin NAFDAC mafi kusa.
Daily Nigerian Hausa

