Jamila Sulaiman Aliyu
Kungiyar Sufaye ta Kasa reshen mata a Jihar Kano ta gudanar da taron Mauludin tunawa da manyan malaman addinin Musulunci da suka bayar da gagarumar gudummawa wajen yada ilimi da kyawawan dabi’u.
Daga cikin malaman da aka tunawa da su akwai Shehu Abdulqadir Jilani, Sheikh Gausullah da kuma Shehu Rasmah, wadanda aka bayyana a matsayin abin koyi ga al’umma, musamman wajen tarbiyya da koyar da addini.
Shugabar Kungiyar Sufaye Mata kuma mai rike da mukamin Naqibatul Kadiriyya, Malama Baraka Adamu Danfanta, ta ce kungiyar na shirya wannan mauludi duk shekara, kuma wannan shi ne karo na goma sha shida da suke gudanar da shi.
Ta bayyana cewa manufar taron ita ce karanta tarihin bayin Allah nagartattu domin ilmantar da mata muhimmancin tarbiyyar ‘ya’yansu, tare da karfafa musu gwiwa su rika kokarin ganin ‘ya’yansu sun zama mutanen kirki da za su amfani al’umma.
Malama Baraka ta ce taron na kuma mayar da hankali wajen jan hankalin iyaye mata kan muhimmancin kula da tarbiyyar ‘ya’ya, musamman a wannan zamani da ake fama da matsalolin lalacewar tarbiyyar matasa.
A cewarta, iyaye mata na taka muhimmiyar rawa wajen gina tarbiyyar ‘ya’ya, domin mafi yawan manyan malaman addini da ake koyi da su sun samu kyakkyawar tarbiyya ne daga iyayensu mata, wadanda suka sadaukar da lokacinsu da basirarsu wajen ganin ‘ya’yansu sun zama abin alfahari.
Ta kara da cewa kungiyar na da burin ci gaba da wayar da kan mata domin taimakawa wajen gyaran tarbiyyar matasa, tare da jaddada cewa idan iyaye suka dauki darasi daga tarihin nagartattun bayin Allah, za a samu sauyi mai kyau a cikin al’umma.
Malama Baraka Adamu Danfanta ta kuma yi kira ga iyaye mata da su sanya ido sosai kan tarbiyyar ‘ya’yansu, domin kaucewa fadawa cikin halaye marasa kyau, tare da tabbatar da sun zama ‘yan kasa nagari masu amfani ga addini da al’umma.

