Hukumar EFCC ta gurfanar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin almundahanar kuɗi da ta kai dala miliyan 2.33.
An gurfanar da Bodejo a gaban mai shari’a Inyang Edem Ekwo kan tuhume-tuhume guda 12 da suka shafi zargin karɓar makudan kuɗaɗen dalar Amurka ba tare da bin hanyar banki kamar yadda doka ta tanada ba.
Gwamnati Ta Kori Ma’aikata Kan Zargin Almundahanan Kudade
Bodejo ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.
Lauyan EFCC, Wahab Shittu (SAN), ya buƙaci kotu ta ci gaba da shari’ar tare da tsare wanda ake zargin, yayin da lauyan Bodejo, Ahmed Raji (SAN), ya nemi a ba shi beli.
Ganduje Ne Ya Sa Aka Kama Ni Saboda Binciken Dukiyar Kano-Muhuyi
Sai dai kotun ta ba da umarnin a tsare Bodejo a ofishin EFCC, sannan ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 20 ga Yulin 2026 domin yanke hukunci kan buƙatar belinsa.
Daily Nigerian Hausa

