Hon. Aliyu Harazimi Rano ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC, wanda hakan ya bashi daga zama dan takarar shugaban karamar hukumar Rano a zaɓen da za a gudanar a ranar 26 ga watan nan.
An dai gudanar da zaben ne a jiya asabar da daddare inda bayan gaza samun masalaha a tsakanin yan takarar aka shiga zaɓen tsakanin yan takara 10.
Read also: Deposed Emir Bayero Guarded by Security At Nasarawa Palace
Bayan kammala kada kuri’u ne Hon. Aliyu Harazimi Rano ya sami nasarar lashe zaɓen da kuri’u tara cikin goma sha shida da aka kada.
Jim kadan bayan lashe zaɓen, jaridar kadaura24 ta zanta da Aliyu Harazimi Rano wanda ya godewa Allah dangane da wannan nasarar da ya samu, Sannan ya godewa shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a karamar hukumar bisa goyon bayan da suka bashi.
Read also: From Vision to Impact: How Comrade Waiya is Redefining Info
“Ina Mika godiya ta musamman ga jagoranmu Dr. Yusuf Jibril JY tsohon kwamishinan gona na jihar kano bisa gudunnawar da yake baiwa jam’iyyar APC don ta sami nasara”.
” Ina kira da dukkanin waɗanda muka yi takarar da su da su zo mu hada hannu wajen guda domin ceto al’ummar karamar hukumar bisa halin da jam’iyyar NNPP ta sanya su a ciki”. Inji Harazimi Rano
Read also: Nigeria Early Warning System: NiMet Unveils 2026–2029 Roadmap
Yace idan yan takarar suka taimaka masa zai iya sami nasarar lashe zaɓen shugaban karamar hukumar ta Rano, don haka yace yana bukatar gudunnawar kowanne daga Cikinsu domin su hada kai don ciyar da karamar hukumar gaba

