Cikin Alhini da juyayi Masarsutar Zazzau take sanar da rasuwan Sarkin Dawakin Zazzau Alhaji Ibrahim Shehu Idris wanda yake Da ne ga Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.
Marigayi Sarkin Dawakin Tsakargida Alhaji Ibrahim ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello wanda ke Shika, Zariya da yammacin yau bayan gajeruwan jinya.
Read also: Hon Chidari Dolles Out Over N40M to Youths in Dambatta, Makoda
Read also: Just In: PDP Loses Another Governor: Delta’s Oborevwori Joins APC
Idan Allah Ya kaimu za a gabatar da Jana’izar Sarkn Dawakin Tsakargidan Zazzau a Gobe Litini da Karfe Goma Sha Daya Na Safiya a Fadan Mai Martaba Sarkin Zazzau.
Read also: NIPHID Develops Curriculum for Diploma in Infectious Diseases
Da fatan Allah Ya jikanshi da rahamanSa, amin.

