Hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta kuɓutar da wasu ‘yan mata 15 waɗanda aka yi yunƙurin safararsu zuwa ƙasashen waje.
Hukumar ta ce an gano yaran ne waɗanda dukkansu ƴan mata ne a tashar mota a cikin birnin Kano.
Read also: Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa Bayan Rikici Tsakanin Matuka
Hisbah Ta Kama Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kawalanci
Rahotanni na cewa masu safarar mutane na amfani da nacewar da ƴan ƙasar ke yi na sai sun fita ƙasashen waje neman rayuwa mai daɗi suna saka su a ƙangin bauna ta zamani.
Hukumar ta HISBA ta ce ta samu wannan nasarar ce yayin wani samame da jami’anta suka kai wata tashar mota.
Kano Hisbah declares suspended Jigawa Commissioner Wanted
Hukumar ta ce yaran masu ƙananan shekaru an kuɓutar da su ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin yin safararsu zuwa Legas.
Read also: Independence Day: Centre Urges Support for Children with Disabilities in Kaduna
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shi ne kwamandan Hisba na Kano ya kuma shaidawa BBC cewa “Mun samu rahoto na wani kamfani da ya yi yunƙurin fitar da mata zuwa ƙasar Saudia, mun kuma miƙa shugabannin kamfanin da muka kama a hannun jami’an hukumar yaƙi da safarar mutane domin gudanar da bincike.”
Hisbah Management Visits Kano State House of Assembly
BBC ta yi ƙoƙarin jin ƙarin bayani daga hukumar ta NAPTIP ofishin jihar Kano, amma haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.
Safarar mutane musamman ƴan mata wata babbar matsala ce da aka jima ana yi a Najeriya.
Kano State Hisbah arrests 14 Over Alleged Betnaija Sports Betting
Kwamared Hafizu Sanka muƙaddashin kodinatan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’Adam ta duniya ofishin jihar Kano, ya ce safarar mutane na ƙaruwa.
Read also: How Katsina’s N3.61bn CDP Is Transforming 361 Wards Through 3,900 Community Projects
“Daga bayanan da muka samu, waɗanda ake safararsu suna shan baƙar wahala, har ma wasu suna tuntuɓarmu don a mayar da su Najeriya.”
BBC HAUSA

