Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin fara aiwatar da manufar “Ba Aiki, Ba Albashi” kan mambobin JOHESU da ke ci gaba da yajin aiki tun daga ranar 14 ga Nuwamba, 2025.
Umarnin ya fito ne ta cikin wata takarda da ma’aikatar kafiya ta tarayya ta fitar a Abuja, wadda aka aikewa da shugabannin asibitocin tarayya, kuma zai fara aiki daga Janairu 2026.
Ma’aikatar ta ce dole ne asibitoci su tabbatar da bin dokar tare da ci gaba da bayar da muhimman ayyukan lafiya kamar kulawar gaggawa, dakunan haihuwa da sassan ICU, har ma da daukar ma’aikatan wucin gadi idan ya zama dole.
Haka kuma, an umurci asibitoci da su bar duk ma’aikatan da ke son ci gaba da aiki su yi hakan ba tare da tsangwama ba, tare da tabbatar da tsaro da aika rahotanni kan tasirin yajin aikin.
Wani kwararre a fannin lafiyar jama’a, Dr. Gabriel Adakole, ya ce duk da cewa matakin yana da tushe a doka kuma na iya kawo karshen yajin aikin, zai iya kara raunana tsarin kiwon lafiyar Najeriya, ganin muhimmancin rawar da mambobin JOHESU ke takawa a asibitoci.
Ya kara da cewa marasa lafiya ne za su fi shan wahala sakamakon jinkirin jiyya da raguwar samun kulawar lafiya, yana mai kira da a yi amfani da tattaunawa da saka jari domin samar da dorewar zaman lafiya a bangaren kiwon lafiya.
Daily Nigerian Hausa

