Mai tsawatarwa marasa rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Ayuba Labaran Kabo, ya miƙa saƙon taya murna ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa zagayowar ranar haihuwarsa da ya cika shekaru 63 a duniya.
Hon. Ayuba Labaran Kabo ya bayyana shekarun Gwamnan a matsayin shekaru masu albarka, yana mai jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zama abin alfahari ga al’ummar Jihar Kano, musamman duba da jajircewarsa wajen gina jihar da kuma aiwatar da manyan ayyukan ci gaba a fannoni daban-daban a faɗin jihar.
Read also: 200 Rice Farms Destroyed as Heavy Rain Hits Kano Community
A cewarsa, irin gagarumin ci gaban da ake samu a Kano ya nuna nagartar shugabancin Gwamnan da kishinsa ga walwalar al’umma.
Read also: Rabies Scare Grips Kano as Dog Bites 18 Residents
Hon. Ayuba Labaran ya ƙara da cewa, a madadin mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano na jam’iyyar APC, suna taya Mai Girma Gwamna murna bisa wannan muhimmiyar rana, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ci gaba da ba shi lafiya, hikima da ƙarfin guiwa domin ci gaba da yi wa al’ummar Kano hidima.
Read also: Kano IntegratE Project Close-Out: Stakeholders Push to Sustain Health Gains
Hakazalika, Hon. Ayuba Labaran Kabo ya jaddada goyon bayan ’yan jam’iyyar APC da ke Majalisar Dokokin Jihar Kano, yana miƙa sakon murna da fatan alheri ga Gwamnan bisa shigowarsa jam’iyyar APC.
A ƙarshe, Hon. Ayuba Labaran Kabo ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su mara wa Gwamna baya domin ƙara ciyar da jihar gaba da tabbatar da dorewar ci gaban da aka fara.

