Sanannen ɗan jarida da mai wasan kwaikwayo, Alhaji Ali Rabi’u Ali, wanda aka fi sani da Daddy, ya zama Shugaban Gudanarwa na tashar Dalla Dalla TV a Kano.
Ali Daddy ya yi fice a fannin jarida da talabijin a Kano, inda ya yi aiki a gidajen rediyo da TV da dama, ciki har da Rahama Radio/TV, Ammasco Radio, da Matashiya TV tun daga shekarar 2014 zuwa 2017. Duk da kasancewarsa ɗan wasan kwaikwayo, ya shahara wajen kiyaye addini da al’adun Hausawa.
Read also: Inside NDLEA’s Dramatic Arrest of Woman Who Hid Tramadol in Fake Pregnancy
Read also: Africa’s Sustainable Dev Tops Agenda at BUK Public Admin Conference
Read also: British-Nigerian Influencer Dies After Penis Enlargement in Thailand
Tashar Dalla Dalla TV, mallakin ƙwararren ɗan jarida Abubakar Adamu Rano, ta zaɓi Ali Daddy ne don jagorantar gidan talabijin, saboda gogewarsa a fannin TV da jajircewarsa a aikinsa.
Ali Rabi’u Ali ya fara aikin shugabancin ne yau, Alhamis 1/1/2026, bayan mika masa ragamar kama aiki.

