Wata kotun yanki da ke zama a Centre-Igboro a Ilorin, jihar Kwara, ta raba auren da ke tsakanin Toyin Ajibola da matarsa, Bashirat Mohammed, sakamakon talauci da mijin ke fama da shi.
Alkalin kotun, Hammad Ajumonbi, ne ya yanke hukuncin bayan Bashirat ta garzaya kotu tana neman a raba aurensu, inda ta koka kan tsananin matsin rayuwa da kuma abin da ta bayyana a matsayin rashin ɗaukar nauyi daga mijinta.
“Ina roƙon kotu ta raba auren nan domin in samu nutsuwar zuciya,” in ji Bashirat a gaban kotu.
Sai dai Ajibola ya shaida wa kotu cewa har yanzu yana son ci gaba da aurensu duk da matsalolin kuɗin da yake fuskanta.
A hukuncinsa, Ajumonbi ya ce duk da cewa Ajibola ya nuna sha’awar ci gaba da aure, bai dace a tilasta wa mace ta ci gaba da zama a auren da ba ta so ba.
Alkalin ya ce Bashirat na buƙatar ci gaba da rayuwarta domin kada ta shiga cikin mawuyacin hali, don haka ya bayar da umarnin raba auren.
Har ila yau, kotun ta umarci Bashirat da ta yi iddah na tsawon watanni uku kafin ta sake yin wani auren.
Daily Nigerian Hausa

