A wani mataki na inganta tsaftar jiki da lafiyar ’yanmata a makarantu, ƙungiyar Bright Capacity Initiative Community Enhancement (BCICE), tare da haɗin gwiwar Plan International, ƙarƙashin shirin ASPIRE Project, ta gudanar da taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki (Roundtable Meeting) kan hanyoyin ci gaba da samar da kayan tsaftar al’ada ga ’yanmata a makarantun Jihar Sokoto
Manufar taron shine a duba hanyoyin da za a samar da sanitary pads (kunzugu) ga ’yanmata a makarantu, domin su samu damar amfani da su a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, tare da tabbatar da cewa shirin ya ci gaba da kasancewa mai ɗorewa ko bayan kammala tallafin da ake samu a halin yanzu.
Da yake bayyana manufar taron, shugaban shirye-shirye na Bright Capacity Initiative Community Enhancement (BCICE) Sanusi Mahmud, ya ce taron ya haɗa masu ruwa da tsaki ne domin tattauna hanyoyin samar da tsarin tallafawa tsaftar al’ada ga ’yanmata a makarantu, da kuma yadda za a tabbatar da dorewar shirin nan gaba.
Ya bayyana cewa ƙarancin kuɗaɗen tallafi da ake samu a halin yanzu ya sa ya zama wajibi a nemi hanyoyin cikin gida da za su taimaka wajen ci gaba da shirin.
A cewarsa, tallafin ƙasashen waje da ake dogaro da shi wajen gudanar da irin waɗannan shirye-shirye ya ragu sosai, lamarin da ya sanya ake buƙatar shawarwari da gudunmawar masu ruwa da tsaki a cikin gida domin samar da hanyoyin samun kuɗaɗen da za su ba da damar ci gaba da tallafawa tsaftar ’yanmata a makarantu.
Ya jaddada cewa shirin Pad Bank muhimmin shiri ne da ke taimakawa wajen rage matsalolin da ’yanmata ke fuskanta a lokacin al’ada, tare da ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da zuwa makaranta ba tare da fargaba ko jin kunya ba.
Ya ƙara da cewa samar da kayan tsaftar al’ada na taimakawa wajen rage kunyatarwa da nuna wariya ga ’yanmata masu jinin al’ada, tare da inganta tsaftar jiki da lafiyar mata.
A nasa ɓangaren, wani jami’i daga Plan International Charls AK ya yi bayani da harshen Ingilishi kan irin gudunmawar da ƙungiyar ke bayarwa ga ƙungiyoyin da ke aiwatar da ayyuka ƙarƙashin shirin ASPIRE Project, musamman wajen inganta lafiyar ’yanmata da samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar ci gaba da karatunsu.
A yayin taron, masu ruwa da tsaki da jami’an gwamnati sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi Pad Bank, da kuma hanyoyin da za a bi domin tabbatar da cewa ’yanmata suna samun kayan tsaftar al’ada cikin sauƙi da kuma a kan lokaci.
Taron ya kuma mayar da hankali kan dabarun da za su bai wa al’umma, hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki damar taka rawa wajen ci gaba da shirin, domin amfaninsa.
Mahalarta taron sun bayyana buƙatar ƙara haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, makarantu da sauran masu ruwa da tsaki, domin samar da ingantaccen tsari na dorewar Pad Bank da sauran shirye-shiryen da ke inganta lafiyar ’yanmata da damar samun ilimi.
VON

