Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), reshen Jihar Kano, ta kammala makon addu’o’inta, inda ta nemi taimakon Allah da shiriya ga jihar Kano da ƙasar Nijeriya baki ɗaya.
Shirin na tsawon mako guda ya haɗa Kiristoci daga mazhabobi daban-daban a fadin jihar Kano, inda aka mayar da hankali kan addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da cigaba.
Read also: Kano Boosts Adolescent Healthcare with 743 Facilities
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya samu wakilci ta hannun Kwamishinan Harkokin Addinai, Ahmad Tijjani Auwalu, wanda ya nuna godiyarsa ga masu shirya taron.
Read also: Girls’ Education: Kano SUBEB, AGILE Distribute 11 Laptops
Ahmad Tijjani Auwalu ya tabbatar wa shugabancin CAN cewa Gwamnatin Jihar Kano na da cikakken ƙuduri na tallafawa duk wani shiri da ke inganta zaman lafiya, haɗin kai da cigaba a jihar.
Da yake jawabi tun da farko, Shugaban CAN na Jihar Kano, Bishop N. Namaza, ya gode wa gwamnatin jihar bisa ci gaba da goyon bayan da take bai wa ƙungiyar, musamman a lokutan ƙalubale.
Read also: Kano Pillars Volleyball Hails Gov Yusuf for Sports Support
Bishop Namaza ya kuma yabawa Kwamishinan Harkokin Addinai, Ahmad Tijjani Auwalu, bisa gaggawar amsawa da kulawa ga bukatun CAN, yana mai bayyana ƙoƙarinsa a matsayin abin a yaba.
Taron ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin addinai da zaman tare cikin lumana a Jihar Kano.

