Mataimakin mai magana da yawun majalisar wakilai, Philip Agbese, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da aiwatar da shirin sauya fasalin Hukumar Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC), yana mai cewa wasu daga cikin sauye-sauyen na iya raunana manufar kafa shirin da kuma rage gudummawar da yake bayarwa ga haɗin kan ƙasa da tsaro.
Agbese, wanda ke wakiltar mazaɓar Ado/Okpokwu/Ogbadibo ta jihar Benue, ya ce duk da cewa akwai buƙatar yin garambawul ga NYSC, ya kamata a fara tattaunawa da ‘yan majalisa, masana harkokin tsaro, tsofaffin jami’an NYSC da sauran masu ruwa da tsaki kafin aiwatar da sauye-sauyen.
FG Approves Technology-Driven NYSC, Risk-Based Deployment
Ya yi adawa da shirin naɗa farar hula a matsayin Darakta Janar na NYSC maimakon jami’in soja, yana mai cewa tsarin soja ya taimaka wajen gina ɗabi’a, kishin ƙasa da ladabtar da matasa.
BUK Issues Guidelines for Batch ‘B’ 2026 NYSC Mobilisation
Kalaman nasa sun biyo bayan sanarwar gwamnatin tarayya ta wasu manyan sauye-sauye ga NYSC, ciki har da raba sansanin horaswa zuwa matakai uku, ƙirƙirar fannonin sana’o’i 11 da masu yi wa ƙasa hidima za su zaɓa, faɗaɗa shirin koyon sana’o’i da kuma maye gurbin kayan khaki da tufafin da ake ƙera a cikin gida.
Daily Nigerian Hausa

