Safiyanu Dantalq
An yi kira ga masu hannu da shuni da su kara zage dantse wajen tallafa wa yara marayu domin inganta rayuwarsu da kuma rage musu radadin rashin iyaye.
Kiran ya fito ne daga bakin Sakataren Hukumar Ilimin Bai-daya (SUBEB) na karamar hukumar Garun Mallam, Alhaji Sabo Muhammad Chiromawa, yayin da ya kai ziyarar gani da ido makarantar marayu ta Garun Mallam Orphans Community Primary School da ke Garun Mallam.
Makarantar, wadda wani tsohon malamin makaranta ke ginawa mai hawa bene, ta samu yabo daga sakataren ilimin, inda ya bayyana aikin a matsayin abin koyi ga al’umma.
Ya ce irin wannan kokari ba kowa ne ke iya yi ba sai wanda Allah Ya hore wa zuciyar taimakon jama’a, musamman marasa galihu da yara marayu.
Alhaji Sabo Muhammad Chiromawa ya kuma bukaci sauran masu hali da su yi koyi da tsohon malamin wajen taimaka wa marayu domin samar da al’umma nagartacciya a nan gaba.
Da yake jawabi, tsohon malamin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa shi kadai ne iyayensa suka haifa, kuma sun ba shi kulawa tare da tabbatar ya samu ilimi tun daga firamare har zuwa jami’a kafin rasuwarsu.
Ya ce duk da rasuwar iyayensa bai hakura da neman ilimi ba, lamarin da ya kai shi ga samun aikin gwamnati har zuwa ritaya.
A cewarsa, hakan ne ya sanya ya kuduri aniyar gina makarantar marayu domin taimaka wa yaran da suka rasa iyayensu da kuma rage musu wahalhalun rayuwa.
Tsohon malamin ya bayyana cewa makarantar na dauke da dakunan karatu masu hawa bene, dakin shan magani, rijiyar burtsatse, dakunan bayan gida na maza da mata da kuma na malamai.
Hakazalika, ya ce an samar da kayan koyo da koyarwa na zamani domin saukaka wa dalibai fahimtar darussa cikin sauki.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ma’aikatar ilimi da su tallafa wajen kammala aikin makarantar, inda ya bayyana cewa an kai kusan kaso 70 cikin 100 na aikin ginin.
Daga cikin wadanda suka raka sakataren ilimin akwai Malam Junaidu Muhammad Chiromawa, Malam Rabiu Yahaya, Malam Abdullahi Gambo Garun Mallam da sauran shugabannin sassan Hukumar Ilimin Bai-daya ta Garun Mallam (LGEA).

