Karamar Hukumar Kumbotso ta samu gagarumar nasara wajen aiwatar da shirin allurar rigakafin shan inna a fadin yankinta, inda aka yi wa yara dubu dari biyu da shida da dari bakwai da uku (200,703) allurar rigakafin, a wani yunkuri na kare lafiyar yara da kawar da cutar shan inna gaba daya.
Manajan Shirin Allurar Rigakafin Shan Inna, Alhaji Badayi Mai Unguwa Rigafada, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da sashen yada labarai na karamar hukumar.
Ya ce nasarar da aka samu ta samo asali ne daga cikakken goyon baya, kulawa da kyakkyawan jagoranci na Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso, Comrade Abdullahi Ghali Basaf, tare da jajircewa da himma ta Shugaban Sashen Lafiya Matakin Farko (PHC), Malam Lawan Ibrahim Ahmad Getso, da dukkan ma’aikatan sashen lafiya.
Alhaji Badayi ya kuma yaba da gudunmawar da abokan hulda a bangaren lafiya suka bayar, ciki har da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), UNICEF da AFENET, inda ya ce hadin gwiwar da aka yi da wadannan kungiyoyi ya taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan nasara.
Haka zalika, Manajan Shirin ya mika godiyarsa ta musamman ga dagatai da masu unguwanni a fadin karamar hukumar, bisa hadin kai, goyon baya da kuma rawar da suka taka wajen wayar da kan al’umma, wanda hakan ya taimaka matuka wajen tabbatar da cewa an cimma burin shirin.
A karshe, ya jaddada bukatar a jinjinawa ma’aikatan wucin gadi da aka dauka domin aiwatar da aikin rigakafin, inda ya bayyana cewa sun nuna kwazo, jajircewa da kwarewa sosai yayin gudanar da ayyukansu, abin da ya taimaka wajen nasarar shirin baki daya.
Karamar Hukumar Kumbotso ta jaddada kudirinta na ci gaba da daukar matakan kare lafiyar yara tare da tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu a bangaren rigakafin cututtuka.

