Hukumar Jin Dadi da Walwalar Alhazai ta jihar Kano ta sanar da Naira Miliyan 8.4 a matsayin wani ɓangare na kuɗin aikin Hajjin baɗi da kowanne maniyyaci zai ajiye.
Shugaban hukumar, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ne ya baiyana hakan yayin wat ganawa da jami’an aikin Hajji na kananan hukumomi a shelkwatar hukumar.
Read also: Gwamnati Ta Kaddamar da Shirin Inganta Tsangayu a Kano
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Suleman Dederi ya fitar a jiya Litinin Kano, Danbappa ya ce Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ce ta bada umarnin a sanar da Naira Miliyan 8.4 a matsayin kason farko na kuɗin aikin Hajjin 2025.
Ya kuma hori maniyyatan da su tabbatar sun biya kudaden su a kan lokaci.
Hakazalika Danbappa ya sanar da cewa NAHCON ta baiwa Kano kason kujerar alhazai 4,356, wanda a cewar sa, za a rarraba su a kananan hukumomi 44 na jihar.
Read also: NEMA Coordinates Response to Gas Plant Fire in Kubwa
Ya kuma sanar da cewa jihar Kano ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin na baɗi, inda ya yi fatan a yi shi cikin nasara.
Read also: Kano IntegratE Project Close-Out: Stakeholders Push to Sustain Health Gains

