Sayyida Bahijja Malam Kabara, ta taya mahaifiyarta, Sayyida Saratu Shaikh Dr. Muhammad Nasir Kabara, murnar karin matsayi da aka yi mata a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.
A cikin wani saƙo da ta wallafa a shafukanta na kafafen sada zumunta, Bahijja ta bayyana farin cikinta da godiya ga Allah bisa karin girman da aka yi wa mahaifiyarta daga Assistant Superintendent of Hisbah II (ASH II) zuwa Assistant Superintendent of Hisbah I (ASH I).
Read also: Girls’ Education: Kano SUBEB, AGILE Distribute 11 Laptops
Ta bayyana karin matsayin a matsayin sakamakon ƙwazo, riƙon amana, jajircewa da sadaukarwar da mahaifiyarta ta yi tsawon shekaru wajen hidimtawa addinin Musulunci, al’umma da kuma Gwamnatin Jihar Kano.
Read also: Kano Boosts Adolescent Healthcare with 743 Facilities
A cewarta, Sayyida Saratu ta shafe sama da shekaru 20 tana aiki a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, tun daga gwamnatin tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau zuwa yanzu, inda take riƙe da muƙamin Mataimakiyar Kwamanda (Mata) ta Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu.
Bahijja ta ce jajircewa, tawali’u da kyakkyawan jagorancin mahaifiyarta sun sanya ta zama abar koyi ga mutane da dama, tare da bayyana cewa sabon karin matsayin ya dace da irin gudunmawar da ta bayar tsawon shekarun aikinta.
Read also: Kaduna Establishes College of Post-Basic Nursing in Rigasa
Ta kuma yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara wa mahaifiyarta lafiya, hikima, ƙarfi da albarka, Ya kuma ba ta ikon ci gaba da sauke nauyin da aka ɗora mata cikin adalci da nasara.
“Allah Ya sanya wannan karin matsayi ya zama mafarin ƙarin ɗaukaka, nasara da lada a duniya da Lahira,” in ji ta.

