Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma Shugaban gidauniyar raya addinin musulunci ta Ganduje ya raba kujerun Hajji da motoci da babura masu kafa uku ga wadanda suka lashe gasar karatun Al-qur’ani sahun farko.
Yayain da sauran wandanda suka lashe gasae suka rabauta da babura masu kafa biyu da kekunan dinki dana hawa da sauran kyaututtuka.
Dr. Ganduje tare Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero sun jagoranci bikin rufe musabaqar Al-Qur’ani mai girma wanda gidauniyar raya addinin musulunci ta Ganduje take daukar nauyi shekara-shekara.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ana shirya Musabaqar ne don zaburar da yara da matasa koyon karatun Qur’ani da bin ka’idojin sa da sanin ma’anar sa da kuma yiwa daliban ilimi kaimi domin su kara maida hankali wajen karatun Qur’ani
Wskilin mu Muhammad Sani ya ruwaito cewa, Manya malamai daga sassa daban-daban na kasa ne da daliban ilimi da sauran muhimman mutane ne suka samu damar halartar taron.
Shugaban kungiyar Izala ta Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau da dan takarar mataimakin gwamnan Kano a shekarar 2023 Alhaji Murtala Sule Garo da Hajiya Asiya Abdullahi Ganduje, Sheikh Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina, na daga cikin wadanda suka mika kyaututtuka ga gwarazan musabaqar
Gidauniyar Ganduje foundation cibiya ce da ta shafe sama da shekaru talatin (30) wajen hidimtawa addinin musulunci da taimakawa al’umma wanda ya hada da gina masallatan juma’a da gina makarantun Islamiyyu da musuluntar da maguzawa da Kuma yiwa masu larurar idanu aiki kyauta