Shugaban Amurka Donald Trump ya yi hasashen cewa yaƙin da ake yi a Iran na dab da kawo ƙarshe, inda ya ce mutane da dama sun fahimci dalilinsa na kawo ƙarshen burin Tehran na mallakar nukiliya.
Shugaba Trump ɗin ya kuma shaida wa manema labarai cewa Iran ta ‘amince’ ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, wani abu da har yanzu Iran ɗin ba ta tabbatar ba.
Read also: Marcus Shines as TYB Lady Captain’s Cup Debuts in Grand Style
Kalamansa na zuwa ne a yayin da Iran ta ce tana nazari kan daftarin da Amurka ta gabatar.
Read also: Polio Vaccine Safe Effective Says Kano Commissioner Of Health
A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Faransa Emmanuel Macron, Shugaba Iran Masoud Pezeshkian ya ce ba za a cimma wata yarjejeniya ba har sai an bayar da tabbacin kawo ƙarshen yaƙin da kuma kawo ƙarshen toshe tashohin jiragen ruwa Iran.
Read also: CARAV Gets New Chairperson, Sets Sights on Eradicating Rape
Rahotanni a kafafen yaɗa labaran Iran sun kuma ruwaito cewa an sake buɗe filin jirgin sama na Tabriz.
BBC HAUSA

