Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Ali Sulaiman Adam, Gadon Kaya, a gaban Babbar Kotun Jihar Kano bisa zarginsa da kashe matarsa, Maryam Nababa Badamasi.
Kunshin tuhumar da gwamnati ta gabatar a kansa ya haɗa da laifin kisan kai da kuma ƙona ɗakin da lamarin ya faru. Bayan an karanta masa tuhumar, Ali Sulaiman ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.
Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Lamido Abba Sorondinki, ya roƙi kotu da ta ba shi lokaci domin fara gabatar da shaidun gwamnati.
A nasa ɓangaren, lauyan wanda ake ƙara, Barista A. A. Dabo, ya nemi kotu ta tabbatar da belin da Babbar Kotun Jihar dake Gezawa ta ba wanda yake karewa a baya. Sai dai kotun ba ta amince da buƙatar nan take ba, lamarin da ya sa lauyan ya nemi a ba shi lokaci domin sake shigar da sabon ƙorafin neman beli.
Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji na Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 15 ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga wannan wata domin duba yiwuwar bayar da beli.
Freedom Radio

