Hukumar tace fina-finai ta Kano ta rufe shagon Kausar Unique Empire Ltd saboda amfani da kalamai da zane-zane na batsa
Sashen Ɗab’i da ke kula da masu sayar da magungunan gargajiya na Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Alh. Abubakar Zakari Garin Babba, ya sanar da nasarar ganowa tare da rufe shagon wata mata da ke tallata magungunan gargajiya a kafafen sada zumunta.
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a, Abdullahi Sani Sulaiman, a madadin Shugaban Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano,
Alh. Abba El-Mustapha, hukumar ta ce matar na tallan magungunan ne cikin salon da ya ƙunshi kalamai tare da zane-zanen abubuwan batsa da suke janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma.
A cewar sanarwar, binciken da hukumar ta gudanar ya tabbatar da cewa shagon mai suna Kausar Unique Empire Ltd, wanda ake yiwa mai shagon lakabi da “Back to Back”, na cikin Jihar Kano.
Ta ƙara da cewa an samu nasarar gano shagon ne bayan samun bayanan sirri daga wasu al’umma masu kishin ci gaban Kano.
Hukumar ta bayyana cewa ta daɗe tana karɓar korafe-korafe daga jama’a kan irin salon tallan da mai shagon ke amfani da shi, wanda ya saɓa wa kyawawan ɗabi’u, tarbiyya da kuma ƙa’idojin zamantakewar al’ummar Jihar Kano.
Hukumar ta jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani nau’in rashin ɗa’a ko karya dokokin da ke jagorantar tallace-tallacen magungunan gargajiya ba, musamman idan ana amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa abubuwan da suka ci karo da ɗabi’u da al’adun al’umma.
Hukumar ta kuma yi kira ga masu gudanar da irin waɗannan kasuwanci da su tabbatar da cewa duk wani tallan da suke yi ya kasance cikin iyakokin dokar Hukumar wanda sukayi daidai da kyawawan ɗabi’un al’ummar Jahar Kano.
Idan zaku iya tunawa, a watannin da suka gabata, Hukumar ta ɗauki irin wannan mataki kan wasu shagunan sayar da magungunan gargajiya da aka samu da laifin karya ƙa’idoji da dokokin Hukumar.

