Gwamnatin Jihar Kano ta samar da magunguna da muhimman kayan aikin asibiti ga Cibiyar Kula da Masu Cutar Makarau (Diphtheria Treatment Unit) da ke Asibitin Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa (IDH) a Kano, domin ƙarfafa ayyukan jinya da inganta kula da marasa lafiya.
Da yake miƙa kayan ga shugabannin asibitin, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta himmatu wajen kare lafiyar al’umma da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a faɗin jihar.
Ya bayyana cewa kayayyakin da aka samar sun haɗa da nau’o’in magunguna, kayan amfani na asibiti (medical consumables), da kayan kariya ga ma’aikatan lafiya, ciki har da rigunan kariya (gowns), domin sauƙaƙa aikin kula da masu cutar makarau.
Dakta Yusuf ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta samar da isasshiyar iskar oxygen ta asibiti (medical oxygen), wadda za a riƙa bai wa marasa lafiya masu buƙata kyauta domin inganta kulawarsu.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar da cewa gwamnati ta shirya tsaf domin tunkarar duk wata barazana ga lafiyar jama’a cikin gaggawa da ƙwarewa.
Kwamishinan ya yabawa ƙungiyar Médecins Sans Frontières (MSF) bisa ci gaba da haɗin gwiwarta da Gwamnatin Jihar Kano wajen inganta ayyukan kiwon lafiya da tallafawa marasa lafiya.
A nasu ɓangaren, wasu marasa lafiya da masu kula da su sun yabawa ma’aikatan lafiya na Asibitin IDH bisa ƙwarewa da jajircewarsu wajen kula da marasa lafiya. Sun kuma jinjinawa gwamnatin jihar da ma’aikatar lafiya saboda samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa, ciki har da wadataccen ruwan famfo da ingantaccen wutar lantarki, waɗanda suka ce sun taimaka wajen inganta ayyukan jinya a asibitin.
Samar da waɗannan magunguna da kayan aiki na daga cikin matakan da Gwamnatin Jihar Kano ke ɗauka na ƙarfafa tsarin kiwon lafiya da kuma yaƙi da yaɗuwar cutar makarau tare da kare lafiyar al’umma.

