Cikin Alhini da juyayi Masarsutar Zazzau take sanar da rasuwan Sarkin Dawakin Zazzau Alhaji Ibrahim Shehu Idris wanda yake Da ne ga Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.
Marigayi Sarkin Dawakin Tsakargida Alhaji Ibrahim ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello wanda ke Shika, Zariya da yammacin yau bayan gajeruwan jinya.
Read also: Sarkin Zazzau Ya Yaba da Gudummawar Queen FM Wajen Wayar da Kan Al’umma
Read also: Nigeria’s Development at Risk Without Girls’ Education- UNICEF
Idan Allah Ya kaimu za a gabatar da Jana’izar Sarkn Dawakin Tsakargidan Zazzau a Gobe Litini da Karfe Goma Sha Daya Na Safiya a Fadan Mai Martaba Sarkin Zazzau.
Read also: BudgIT, Malala Fund Tackle Barriers to Girls’ Education in Kano
Da fatan Allah Ya jikanshi da rahamanSa, amin.

