Hukumar EFCC ta jaddada cewa dole ne a ci gaba da sauraron shari’ar tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, tare da ‘ya’yansa da sauran waɗanda ake tuhuma, a gaban alkaliyar da ta fara shari’ar, Ijeoma Ojukwu.
Lauyan EFCC, Chile Okoroma, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a gaban Peter Lifu a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Ya ce har yanzu hukumar na jiran martanin Babban Alkalin Kotun Tarayya, John Tsoho, kan buƙatar da suka gabatar.
Okoroma ya yi wannan bayani ne bayan an kira karar domin sake gurfanar da waɗanda ake tuhuma, inda ya bayyana cewa buƙatar EFCC ta yi daidai da umarnin da Kotun Koli ta bayar.
Ya ƙara da cewa, a zaman da ya gabata sun sanar da kotu cewa sun rubuta wa Babban Alkalin Kotun Tarayya wasika, suna neman a bai wa Mai shari’a Ojukwu izini na musamman domin ta ci gaba da sauraron shari’ar, duk da cewa yanzu tana aiki a reshen kotun da ke Calabar.
A cewarsa, tun da masu gabatar da ƙara sun riga sun gabatar da shaidu akalla 17, akwai buƙatar alkaliyar da ta fara shari’ar ta kammala ta.
Daga nan sai ya roƙi kotu da ta ɗage zaman domin jiran sahihin martani daga ofishin Babban Alkalin Kotun Tarayya.
A nasa ɓangaren, lauyan waɗanda ake ƙara, Joe Agi, bai nuna adawa da wannan buƙata ba.
Mai shari’a Lifu ya amince da buƙatar, inda ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 30 ga Afrilu domin sake gurfanar da waɗanda ake tuhuma ko ɗaukar wasu matakan shari’a.

