Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB), Malam Yusuf Kabir, ya sake jaddada kudirin Hukumar na ci gaba da inganta harkokin koyo da koyarwa a faɗin jihar, ta hanyar managartan shirye-shiryen da ke ƙarfafa ɗalibai su riƙa zuwa makaranta da wuri kuma akai-akai.
Shugaban Hukumar ya bayyana haka ne a yayin ziyarar da ya kai Makarantar Sabilu Sa’adah Islamiyya da GGJSS Sabo Garba Community School, waɗanda dukkansu suke Unguwar Dorayi da ke ƙarƙashin Gwale LGEA a Jihar Kano, inda aka ba ɗaliban da suka zo makaranta da wuri kyaututtuka domin yaba musu bisa jajircewarsu wajen zuwa makaranta akan lokaci.
Read also: Kano Signs MoU with IBP on Health Financing Dashboard
Da yake magana a yayin ziyarar, Malam Yusuf ya jaddada cewa zuwa makaranta da wuri na daga cikin muhimman abubuwan da ke taimakawa wajen samun ingantaccen koyo da koyarwa, musamman a lokutan safiya, lokacin da ake koyar da muhimman darussa. Ya kuma tabbatar da cewa zuwan dalibai makaranta da wuri na taimakawa matuƙa wajen inganta sakamakon karatu, da habbaka fahimtar darussa da kuma gina kyakkyawar ɗabi’a game da neman ilimi.
Ya bayyana cewa wannan shirin yana baiwa Hukumar damar tantace yadda makarantu ke kula da lokacin zuwa makaranta, tare da karfafa guiwar daliban da suka saba zuwa makaranta da wuri.
Read also: Northwest Safe School Summit: Stakeholders Call for Action, Accountability
A wani ɓangare na wannan shiri, ɗalibai 50-50 ne suka rabauta da kyaututtukan daga kowace makaranta, inda suka sami, jakar makaranta da takalmi da littattafan rubutu guda 12 da fensir guda 12, domin karramasu bisa jajicewarsu wajen zuwa makaranta da wuri da kuma halartar makaranta akai-akai.
Haka kuma, malamai shida daga makarantun biyu sun rabauta da bashin sayen abin hawa mara ruwa, domin taimaka musu wajen rage musu nauyin matsalolin tattalin arziki, da kuma kyautata musu musamman bisa yadda suke kiyaye zuwa wurin aiki akan lokaci.
Shugaban Hukumar ya buƙaci waɗanda suka amfana da kayan karatun da su yi amfani da su yadda ya kamata, tare da ci gaba da kasancewa masu ladabi da kiyaye lokaci da kuma mayar da hankali wajen karatunsu. Ya kuma yi kira ga iyayen yara da su mara wa Hukumar baya ta hanyar tabbatar da cewa ’ya’yansu suna zuwa makaranta akai-akai kuma akan lokaci a kowace rana.
Read also: Kano: Group Raises Alarm Over Emir’s Alleged Rally
Ɗaliban da suka amfana da tallafin sun nuna godiyarsu ga Shugaban Hukumar bisa wannan gudunmawa, inda suka bayyana cewa kyautar ta ƙara musu ƙwarin gwiwar ci gaba da zuwa makaranta da wuri da kuma jajircewa wajen neman ilimi.
Sun kuma yi alkawarin yin amfani da kayan da aka ba su yadda ya kamata, tare da ci gaba da zuwa makaranta da wuri kuma akai-akai ba tare da fashi ba.

