Gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Tinubu ta shirya dawo da tallafin man fetur na tsawon wata daya ta hanyar rage farashin man fetur na tsawon wata ɗaya
Gwamnatin Tarayya ta bayyana wani sabon shiri da zai bai wa ‘yan Najeriya damar sayen man fetur a farashi mai rahusa na tsawon kwanaki 30.
Read also: Katsina: Mutane 5 Masu Muƙaman Siyasa Sun Yi Murabus
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa za a fara sayar da man fetur a farashi mai sauƙi a gidajen mai na NNPC, a wani mataki da ake sa ran zai rage wa al’umma radadin tsadar man fetur da kuma hauhawar farashin sufuri.
Read also: OPEN LETTER TO HIS EXCELLENCY, PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU
Gwamnatin ta ce shirin zai ɗauki tsawon wata guda, inda ‘yan Najeriya za su samu damar amfana da rangwamen farashin man fetur a wannan lokaci.
Read also: Tinubu’s Renewed Hope Will Drive Investment, Growth-Minister
Ana sa ran matakin zai taimaka wajen rage matsin tattalin arziki da ke damun al’umma, musamman masu amfani da motocin haya da sauran masu buƙatar man fetur a kullum.
Mikiya

