Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance, lamarin da ya haifar da gagarumin sauyin siyasa a jihar Kano, inda ’yan Majalisar Dokoki 34, shugabannin kananan hukumomi 44, da kuma dukkan tsarin masu rike da mukaman siyasa suka bi sahunsa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani gagarumin biki da aka gudanar a Coronation Hall na Fadar Gwamnatin Jihar Kano.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Yusuf ya ce ficewar ta biyo bayan tattaunawa mai zurfi da kuma yin nazari kan halin da jihar Kano ke ciki a yanzu da kuma burinta na gaba.
Ya bayyana cewa matakin ya zama dole domin yin aiki kafada da kafada da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, domin hanzarta ci gaban jihar tare da tabbatar da amfanin dimokuradiyya ga al’ummar Kano.
“Bayan shawarwari masu fadi da zurfin tunani kan makomar jihar Kano, ni tare da ’yan Majalisar Dokoki 34, shugabannin kananan hukumomi 44 da dukkan masu rike da mukaman siyasa, mun yanke shawarar shiga jam’iyyar APC domin yin aiki tare da shugabancin hangen nesa na Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu,” in ji Gwamnan.
Gwamna Yusuf ya kara da cewa Ajandar Renewed Hope ta Shugaban Kasa na haifar da sakamako mai kyau a fadin kasa, yana mai jaddada cewa Kano ba za ta iya ci gaba da kasancewa a gefe ba, musamman a lokacin da hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya zai iya samar da karin dama ga al’ummarta.
Ya ce rikice-rikicen siyasa da takaddama ba sa haifar da kyakkyawan shugabanci, yana mai bayyana cewa shugabanci nauyi ne da ya kamata ya ta’allaka kan aikin yi wa al’umma hidima, ba fafatawa ba.
“Mulki nauyi ne kuma yana bukatar sakamako. Ta hanyar hada Kano da Gwamnatin Tarayya, mun zabi ci gaba fiye da girman kai,” in ji shi.
Gwamnan ya tabbatar wa magoya bayansa cewa wannan mataki ba zai rage darajar sadaukarwa da gudunmawar wadanda suka mara masa baya tsawon tafiyarsa ta siyasa ba.
Ya bukaci al’ummar Kano da su duba wannan sauyi cikin adalci da fahimta, yana mai jaddada cewa an dauki matakin ne cikin kyakkyawar niyya domin samar da karin damammaki, musamman ga matasa masu yawan gaske a jihar.
Gwamna Yusuf ya sanar da amincewa da kafa Majalisar Dattawan Kano, wacce zai kasance ba ta bangaranci ba, kuma za ta rika ba gwamnati shawara domin karfafa zaman lafiya, hadin kai da kyakkyawan shugabanci.
A cewarsa, hadewar da Gwamnatin Tarayya zai taimaka wajen samar da yanayi mai tsafta da kwanciyar hankali a fagen siyasa, tare da inganta hadin kai da dorewar zaman lafiya.
“Mun bude sabon babi ne bisa hadin kai, kwanciyar hankali da shigar kowa cikin harkokin mulki. Kofofinmu a bude suke ga dukkan al’ummar Kano,” in ji Gwamnan, yana mai yabawa shugabannin APC bisa goyon baya da halartar bikin ficewar a hukumance.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da suka halarci taron sun hada da tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Kasa, Sanata Barau Jibrin; Karamin Ministan Gidaje da Cigaban Birane, Abdullahi Ata Fagge; Sanata Kawu Sumaila; Shugaban Jam’iyyar APC a Kano, da kuma dukkan shugabannin kananan hukumomi 44, tare da sauran manyan ’yan jam’iyya.

